Jump to content

Saki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Saki
Matsayin aure
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na rushewa, separation (en) Fassara, end cause (en) Fassara da muhimman sha'ani
Mabiyi married (en) Fassara da legal separation (en) Fassara
Has cause (en) Fassara marital breakdown (en) Fassara da breakup (en) Fassara
Has immediate cause (en) Fassara sham marriage (en) Fassara
Yana haddasa divorcee (en) Fassara
Hannun riga da Aure
Biertan house for divorcing people
Celebrating divorce
yanda wasunsuka raba aurensu

Saki, ana kiransa da warwarewar aure, shi ne hanyar da ake bi wurin kawo karshen zaman takewar aure.[1] Ya haɗa da sokewa ko sake fasalin iko da nauye-nauyen dake cikin aure, da rushe dangantakar da take tsakanin ma'aurata a karkashin dokar wata kasa ko jiha[2]. Dokokin saki sun banbanta a kasashen duniya,[1] amma a mafi yawan kasashe, saki na bukatar tabbacin kotu ko na wasu hukumomi da aka amince da su na doka, wanda ya hada da abubuwa kamar rarraba kayayyaki,[3] wurin zaman da,[3] alimony (taimakon aboki/abokiyar zama), ziyartan da / access, lokacin iyayentaka, taimakon da, da raba bashi. A yawancin kasashe, auren mace daya (monogamy) aka amince da shi a doka, haka ya sa bayan saki ma'auratan kan iya auren wanda suke so daga baya; amma a auren mace fiye da daya (polygamy) an yarda sai dai ba'a yarda da mace ta auri miji fiye da daya (polyandry) ba, saki na sa mace ta auri wanda take so.

Saki ba daya yake da kashe-aure ba, wanda ke tabbatar da cewa aure bai yi ba kuma bai halatta, tare da rabuwar ko de jure.

Sai dai akwai kasashen da ba su yarda da saki ba bayan an yi aure, kasashen kuwa su ne; Philippines, Birnin Vatica da kuma British Crown Dependency na Sark.[4] a kasar Philippines, saki ga wadanda ba-Musulmai ba Filipinos ba halas ba ne sai dai idan mijin ko matar ba 'yar kasa ba ce kuma sun cika wasu sharudda.[5] amma a birnin Vatica, ita jiha ce ta ikilisiya (ecclesia), wanda ba shi da wani hanyar yin saki. Kasashen da suka amince da Saki ba da dadewa ba su ne; Italy (1970), Portugal (1975), Brazil (1977), Spain (1981), Argentina (1987),[6] Paraguay (1991),[7] Colombia (1991*[7][8]), Andorra (1995),[9] Ireland (1996), Chile (2004)[10] da kasar Malta (2011).

Madauci, Ibrahim. (1968). Hausa customs. Isa, Yahaya., Daura, Bello. [Zaria]: Northern Nigerian Pub. Co. ISBN 978-169-097-6.OCLC 489903061.

  1. 1.0 1.1 "Divorce". Encyclopaedia Britannica.
  2. Madauci, Ibrahim. (1968). Hausa customs. Isa, Yahaya., Daura, Bello. [Zaria]: Northern Nigerian Pub. Co. pp.310. ISBN 978-169-097-6.
  3. 3.0 3.1 "Family law". Encyclopaedia Britannica. |section= ignored (help)
  4. Kaushik (2013-08-17). "Isle of Sark: Europe's Last Feudal State". Amusing Planet. Retrieved 2017-05-13.
  5. Gloria, Charmian K (2007). "Who needs divorce in the Philippines?". Mindanao Law Journal. 1: 18–28.
  6. "Divorce Is Now Legal in Argentina but, So Far, Few Couples Have Taken the Break". Los Angeles Times.
  7. 7.0 7.1 Sex and the State: Abortion, Divorce, and the Family Under Latin. American Dictatorships and Democracies, by Mala Htun, pp 102
  8. Divorce between 1976 and 1991 was allowed only for non-Catholics.
  9. Le divorce en droit comparé: Europe by Bernard Dutoit, Raphaël Arn, Béatrice Sfondylia, Camilla Taminelli, pp.56
  10. "Chile introduces right to divorce". BBC News. BBC. November 18, 2004. Retrieved 2013-11-01.
  翻译: